Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaAn warware rikicin rijiyar mai ta OPL 245 - Gwamnatin Nijeriya

An warware rikicin rijiyar mai ta OPL 245 – Gwamnatin Nijeriya

Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, ya ce warware rikicin rijiyar mai ta OPL 245 zai taimaka wajen farfado da tattalin arzikin Nijeriya da kuma karfafa kudaden shiga na gwamnati.

Ya bayyana hakan ne bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar da ta kawo karshen rikicin da ya shafe sama da shekaru 20, tsakanin gwamnatin tarayya da kamfanonin Eni da Nigerian Agip Exploration Limited a Abuja.

Fagbemi ya yabawa shugaba Bola Ahmed Tinubu kan jagoranci da ya nuna wajen bada umarnin a warware rikicin cikin lumana domin amfanin al’ummar Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata