Babban hafsan sojin Uganda, wanda ɗan Shugaba Yoweri Museveni ne da aka sake zaɓa, ya bayyana cewa mutane 30 daga magoya bayan ‘yan adawa sun mutu, yayin da sama da mutum 2,000 aka kama, biyo bayan zaɓen ƙasar.
Shugaban sojin, Muhoozi Kainerugaba, ya bayyana hakan ne a ranar Jumma’a, bayan zaɓen da aka gudanar a 15 ga Janairu.
Jaridar Punch ta rawaito cewa a halin yanzu, jagoran ‘yan adawa Bobi Wine na ɓoye, bayan da ya zargi jami’an tsaro da kai hari gidansa bayan kammala zaɓen,bayan ya bayyana kin amincewarsa da sakamakon zaben.
