Wednesday, April 8, 2026
HomeLabaraiAn yi nasarar a yaki da rashin tsaro

An yi nasarar a yaki da rashin tsaro

Ministan Tsaron Nijeriya, Mohammed Abubakar Badaru, ya ce nasarorin da sojoji suka samu a baya-bayan nan na nuni da cewa Nijeriya ta tunkari magance matsalar tsaro.

Ministan ya ce a karon farko cikin shekaru, ‘yan Nijeriya na iya tafiya hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna ko da cikin dare, Zaria zuwa Funtuwa zuwa Gusau yanzu an samu zaman lafiya, kuma titin Abuja zuwa Kaduna ya samu tsaro.

Badaru Abubakar ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da manema labarai.

Daily Nigerian ta rawaito cewa Badaru ya ce Shugaba Bola Tinubu ya ba da umurnin kawo karshen rashin tsaro da da wuri kafin karshen 2025.

Ya yi nuni da Operation Fasar Yamma da sauran kokarin da sojoji ke yi a wurare daban-daban a fadin kasar nan a matsayin jami’an da ke kokarin samar da ingantaccen tsaro a yankuna da dama.

Badaru ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu dai an samu nasarar kashe ‘yan ta’adda 13,543 da ‘yan fashi, an kama 17,500, an ceto mutane 9,821 da aka yi garkuwa da su, sannan ‘yan ta’adda 24,000 sun mika wuya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata