Monday, April 6, 2026
HomeKetareAn yi wa madugun adawar Uganda Bobi Wine daurin talala yayin da...

An yi wa madugun adawar Uganda Bobi Wine daurin talala yayin da Shugaba Museveni ke kan gaba a zaben da ya gudana a kasar

Jami’an tsaro a Uganda sun tsare jagoran adawa Bobi Wine a gidansa, kwana guda bayan gudanar da zaɓen shugaban ƙasa, yayin da sakamakon farko ke nuna Shugaba Yoweri Museveni na kan gaba sosai.

Hukumar zaɓe ta Uganda ta ce bayan kidayar kusan kashi ɗaya cikin huɗu na ƙuri’u, Museveni ya samu kashi 76.25, yayin da Bobi Wine ya samu kashi 19.85, a zaɓen da ake sa ran za a fitar da sakamakonsa na ƙarshe da safiyar Asabar.

Jam’iyyar Bobi Wine, National Unity Platform, ta ce jami’an tsaro sun kewaye gidansa tare da hana shi fita, inda suka bayyana matakin a matsayin tsare shi a gida ba bisa ƙa’ida ba, yayin da ‘yan sanda da sojoji suka mamaye yankin.

Zaɓen dai ya gudana ne cikin matsin lamba, matsalolin injinan tantance masu zaɓe, da kuma katse intanet a faɗin ƙasar, lamarin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ya nuna yanayi na tsangwama da tsoratarwa ga ‘yan adawa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata