Kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ya sanar da rufe matatar mai ta Fatakwal (PHRC) daga ranar Asabar domin gudanar da gyare-gyare da duba lafiyar aikin injina a matatar.
Wannan na zuwa watanni shida bayan fara aikin dakon mai daga matatar bayan kashe dala biliyan 1.5 wajen gyaranta.
Jami’in hulɗa da jama’a na NNPCL, Femi Soneye, ya ce rufewar na cikin tsare-tsaren kiyayewa da tabbatar da ingancin aiki a matatar.
Masana masana’antu da wasu masu ruwa da tsaki sun nuna damuwa, suna kuma kira da a sayar da matatun gwamnati gaba ɗaya don samun inganci da cikakken amfanin su ga Nijeriya.
