Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiAna fargabar mutane da dama sun nutse sanadiyyar kifewar jirgin ruwa a...

Ana fargabar mutane da dama sun nutse sanadiyyar kifewar jirgin ruwa a Neja

Rahoton jaridar The Nation ya ce mutane da dama, ciki har da mata da yara, sun rasu yayin da wani karamin jirgin kwale-kwale na katako ya nutse a kogin Shiroro da ke karamar hukumar Shiroro a Jihar Neja a ranar Asabar.

Wani ganau ya bayyana cewa jirgin ya taso daga Guni yankin rafi a karamar hukumar Munya zuwa kasuwar Asabar da ke ci a Zumba, inda ya nutse da misalin karfe 2:30 na rana bayan ya ci karo da wata bishiya da ke cikin ruwa.

Rahotanni sun ce an makare jirgin da fasinjoji da kaya, saidai ana ci gaba da aikin ceto, amma har yanzu ba a san yawan adadin wadanda suka rasu ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata