Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaAna zargin tsohon ministan tsaro Badaru na shirin barin APC

Ana zargin tsohon ministan tsaro Badaru na shirin barin APC

Tsohon gwamnan Jigawa kuma tsohon ministan tsaro, Muhammed Badaru Abubakar, na fuskantar jita-jitar cewa zai iya barin jam’iyyar APC.

Hakan ya biyo bayan rashin ganinsa a taron jam’iyyar APC a jihar da kuma ganawarsa da wasu ‘yan adawa kamar Sule Lamido da Mustapha Lamido.

Kodayake jaridar Daily Trust ta ambato Badaru ya musanta shirin sauya jam’iyya, yana cewa ganawar da aka gani na iya kasancewa ne kawai a matsayin ziyara ko tuntuba.

Gwamnatin jihar karkashin ta bakin mai magana da yawun gwamna Umar Namadi, Hon. Hamisu Gumel ta ce ko da Badaru ya bar jam’iyyar, APC ba za ta rasa karfinta ba a jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata