Jam’iyyar APC a jihar Kebbi ta dakatar da shugaban karamar hukumar Birnin Kebbi kuma shugaban Ciyaman ALGON na jihar Dahiru Nayaya daga jam’iyyar bisa zargin aikata rashin da’a da saba wa ka’ida.
Dakatarwar na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mataimakin shugaban APC na yankin Kebbi ta Tsakiya Abubakar Bello ya aikewa manema labarai.
A cewar takardar, jam’iyyar ta dauki matakin ne bayan samun rahotannin binciken cikin gida, wadanda suka danganta Dahiru Nayaya da yin wasu ayyukan da jam’iyyar ta ce suna barazana ga hadin kai da martabar APC.
