Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiAPC ta lashe zaben daukacin kananan hukumomin jihar Lagos

APC ta lashe zaben daukacin kananan hukumomin jihar Lagos

Jam’iyyar APC ce ta lashe dukkan kujerun shugabancin kananan hukumomi guda 20 a zaben kananan hukumomin da aka gudanar a jihar Legas.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Legas (LASIEC) ce ta bayyana hakan a ranar Lahadi, inda ta ce APC ta kuma samu nasara a kujeru 375 daga cikin 376 na kansiloli a fadin jihar.

Jam’iyyar PDP ce kawai ta samu kujera guda daya ta kansila a mazabar Ward D, Yaba.

A ranar Asabar ne aka gudanar da zaben, inda masu kada kuri’a a jihar suka fito domin zaben shugabannin da za su jagoranci kananan hukumomi 20.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata