Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaAPC ta musanta ba 'yan majalisar dokokin Nijeriya tikitin takara na yin...

APC ta musanta ba ‘yan majalisar dokokin Nijeriya tikitin takara na yin tazarce babu hamayya a 2027

Jam’iyyar APC ta musanta rahotannin da ke yawo a kafafen yada labarai da ke cewa ta bai wa dukkanin ’yan majalisar tarayya da ke kan kujeru tikitin tsayawa takara don tazarce ba tare da hamayya ba, tana bayyana irin wannan labari a matsayin “marar tushe bare makama.”

A wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na kasa, Felix Morka, ya fitar, jam’iyyar APC ta bukaci ’ya’yanta da al’umma gaba daya da su yi watsi da abin da ta kira “rahoton karya da ake ikirarin ya fito daga jam’iyyar.”

Wannan bayani ya fito ne a daidai lokacin da ake kara yada jita-jita game da tsarin zaben fitar da ’yan takarar jam’iyyar gabanin zabe mai zuwa.

Morka ya jaddada cewa duka hukuncin da jam’iyyar za ta yanke za a sanar da su ne ta hanyoyi na hukuma da aka tabbatar da sahihancinsu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata