Jam’iyyar APC ta bayyana cewa duk wanda ke son tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 sai ya biya jimillar kuɗi miliyan 100 domin sayen fom ɗin nuna sha’awa da na tsayawa takara, lamarin da ya janyo cece kuce a fagen siyasar Nijeriya.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa jam’iyyar ta fitar da jadawalin shirye-shiryen zaɓen fidda gwani, wanda Sakatare na shirye-shirye na ƙasa, Sulaimon Arugungu, ya fitar, inda aka bayyana cewa masu neman takarar shugaban ƙasa za su biya miliyan 30, na fom ɗin nuna sha’awa da kuma miliyan 70 na fom ɗin tsayawa takara.
Haka kuma, masu neman gwamna za su biya miliyan 50 gaba ɗaya, yayin da na majalisar dattawa da wakilai da kuma na jihohi suma aka ware musu kudade daban-daban.
Baya ga haka, jam’iyyar ta tsara cewa sayar da fom zai fara daga ranar 25 ga Afrilu zuwa 2 ga Mayu, sannan ranar ƙarshe na miƙa fom ita ce 4 ga Mayu, 2026.
