Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiAPC ta talauta ‘yan Nijeriya fiye da kowace gwamnati a tarihin kasar...

APC ta talauta ‘yan Nijeriya fiye da kowace gwamnati a tarihin kasar – Shugabar riko ta jam’iyyar LP

Shugabar rikon kwarya ta jam’iyyar Labour Party, Sanata Nenadi Esther Usman, ta ce jam’iyyarta tana da shirin gyara kura-kuran da gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki ta tafka, wadda ta bayyana da cewa ta gaza matuka.

Yayin da take zantawa da manema labarai a jihar Kaduna dangane da abubuwan da ke gudana a cikin jam’iyyar LP, Sanata Nenadi ta bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da bada goyon baya ga jam’iyyar, tana mai cewa LP za ta ci gaba da zama sahihin zabi mai mayar da hankali kan talakawa, domin dawo da fata da martabar kasa.

A cewarta, gwamnatin APC ta “talauta ‘yan Najeriya fiye da kowace gwamnati a tarihin kasar,” inda ta bayyana halin rayuwa a kasar a yau da cewa “ba za a iya jurewa ba.”

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata