Jam’iyyar APC ta yi nasara a zaɓen cike gurbi da aka gudanar a kananan hukumomin Ghari da Tsanyawa na jihar Kano.
Babban jami’in zaɓen yankin, Farfesa Muhammad Waziri daga Jami’ar Bayero Kano, ya ce ɗan takarar APC, Garba Ya’u Gwarmai, ya samu ƙuri’u 31,472, inda ya kayar da abokin hamayyarsa na jam’iyyar NNPP, Yusuf Ali Maigado, wanda ya samu ƙuri’u 27,931.
Sakamakon ya tabbatar da dawowar Garba Ya’u Gwarmai, wanda a baya shi ne ɗan majalisar jiha mai wakiltar Ghari da Tsanyawa.
An gudanar da wannan zaɓen ne bayan hukumar zaɓe ta soke wanda aka yi a baya tare da bayyana shi a matsayin wanda bai kammala ba.
