Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiASUU ba ta da hujjar shiga yajin aiki domin mun biya dukkanin...

ASUU ba ta da hujjar shiga yajin aiki domin mun biya dukkanin bukatunta – Gwamnatin Nijeriya

Gwamnatin tarayya ta roƙi kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU da ta dakatar da yajin aikin da ta fara, tana mai cewa ta cika dukkan bukatun da kungiyar ta gabatar kuma ta mika mata sabon tayin yarjejeniya.

Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya bayyana hakan ne a hirar da aka yi da shi a tashar Channels TV a ranar Litinin, inda ya ce gwamnati ta tattauna da ASUU sau da dama tun bayan karɓar mukaminsa, don haka babu hujjar ci gaba da yajin aiki.

Alausa ya ce, sun biya dukkan bukatun ASUU ɗaya bayan ɗaya, ba dalilin yajin aikin nan don haka muna roƙonsu da su koma makaranta kamar yadda Punch ta ruwaito.

Sai dai a ranar Lahadi ASUU ta sanar da fara yajin aikin gargadi na makonni biyu a dukkan jami’o’in gwamnati, tana mai zargin gwamnatin tarayya da kin cika alkawuran da ta dauka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata