Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiASUU ta bai wa gwamnatin Najeriya wa'adin makonni biyu

ASUU ta bai wa gwamnatin Najeriya wa’adin makonni biyu

Kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya ASUU ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin makonni biyu don biya mata bukatunta.

Kungiyar ta dauki matakin ne biyo bayan wani taron majalisar zartaswa da ta gudanar a Abuja, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.

Wata sanarwa da shugaban kungiyar Farfesa Chris Piwuna ya sanya wa hannu, ta koka da yadda ta ce gwamnatin na yawan yin watsi da al’amuran da suka shafi kungiyar, da ma sauran harkokin jami’o’i a Najeriya.

A cewar sa, muddin wa’adin ya kare gwamnati ba ta dauki matakin da ya dace ba, babu wani zabi da ya wuce ta tsunduma yajin aikin gargadi na makonni biyu, daga nan kuma ta fara na sai baba ta gani.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata