Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiASUU ta yi sabon ango, Chris Piwuna ya zama sabon shugaban kungiyar...

ASUU ta yi sabon ango, Chris Piwuna ya zama sabon shugaban kungiyar malaman jami’o’i ta Nijeriya

Kungiyar malaman jami’o’i ta Nijeriya ASUU ta zabi Farfesa Chris Piwuna, kwararren likitan kwakwalwa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos, a matsayin sabon shugabanta na kasa.

Farfesa Piwuna, wanda kuma shi ne shugaban sashen kula da harkokin dalibai sato Dean Student Affairs a Jami’ar Jos, ya karbi ragamar shugabancin daga hannun Farfesa Victor Osodeke, masani a fannin kimiyyar kasa daga Jami’ar Noma ta Michael Okpara da ke Umudike, Jihar Abia.

An yanke wannan hukunci ne a yayin babban taron zaben sabbin shugabannin kungiyar na kasa karo na 23, da aka gudanar a garin Benin na jihar Edo.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata