Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaAtiku Abubakar ya yi fatali da matakin gwamnonin PDP na kin amincewa...

Atiku Abubakar ya yi fatali da matakin gwamnonin PDP na kin amincewa da yin haɗaka

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya dage cewa hadin gwiwa tsakanin jam’iyyu ita ce kawai hanyar da za su iya kayar da shugaban kasa Bola Tinubu a zaben 2027.
Atiku ya nuna adawa da matsayin gwamnonin jam’iyyar PDP wadanda suka nisanta jam’iyyar daga kawancen da tsohon mataimakin shugaban kasar ke shirin yi.
A ranar Litinin, kungiyar gwamnonin PDP karkashin jagorancin gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, sun bayyana cewa jam’iyyar ba za ta shiga cikin wata hadaka da kowace jam’iyya ba.
Sai dai a martanin da ya mayar, Atiku Abubakar ta hannun mataimakinsa kan yaɗa labarai Paul Ibe, ya jaddada bukatar fadada tattaunawa domin samun tattaunawa.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata