Ministar Al’adu, Fasaha da Kirkira, Hannatu Musawa, ta ce tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ba zai iya doke Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027 ba, ko da ya haɗu da Peter Obi a tikitin zaɓe ɗaya. Ta bayyana hakan ne a wata hira da aka wallafa a shafin Instagram na TheMicon Podcast.
Musawa ta ce duk da cewa Atiku mutum ne mai ƙarfi a siyasa, ba ta ganin zai iya kayar da jam’iyya mai mulki. Ta ƙara da cewa haɗin Atiku da Peter Obi zai janyo rarrabuwar kai a cikin magoya bayan Obi, inda da dama ba za su amince Obi ya tsaya matsayin mataimaki ba kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Ta kuma yi gargaɗin cewa idan har Peter Obi ne zai zama ɗan takarar shugaban ƙasa a irin wannan haɗin gwiwa, hakan zai ƙara raunana damar adawa. Kalaman nata sun haifar da muhawara a kafafen sada zumunta yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.
