Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar, ya kai ziyara ta musamman ga tsohon ministan shari’a Abubakar Malami, domin jajanta masa bisa harin da aka kai wa ayarin motocinsa a Birnin Kebbi.
Atiku, wanda guda ne daga cikin manyan shugabannin jam’iyyar hadaka ta ADC, ya bayyana damuwa kan yadda ake samun hatsaniya tare da zargin kai wa fitattun jiga-jigan jam’iyyar hari a jihohi daban-daban na ƙasar.
A cikin wata sanarwa da kodinetan shiyya na kungiyar da ke goyon bayan Malami, Muhammad Al-Amin ya fitar, Atiku ya ce ya zama wajibi shugabanni su haɗa kai wajen dakile waɗannan kai hare-hare da suka kira na “adawa da dimokuraɗiyya.”
Ya jaddada cewa jam’iyyar ADC ta ƙuduri aniyar kare ƙasar daga duk wata barazana da ka iya haddasa durƙusar da tsarin dimokuraɗiyya.
