Tsohon dan takarar shugabancin Nijeriya, Atiku Abubakar, ya shiga tsakani domin kwantar da tarzoma bayan takaddama ta kaure tsakanin magoya bayansa da na tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi, kan tikitin shugaban kasa na jam’iyyar ADC gabanin zaben 2027.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa rikicin ya karu ne bayan Peter Obi ya fice daga jam’iyyar Labour Party zuwa ADC a watan Disambar 2025, inda ya bayyana cewa ya dauki matakin ne domin gina hadakar adawa mai karfi da za ta iya fuskantar matsalolin tattalin arzikin Nijeriya da kuma kayar da jam’iyyar APC mai mulki.
Tun bayan shigar Obi cikin hadakar, magoya bayansa musamman ‘yan Obidient Movement suka kara matsin lamba ga Atiku da ya goyi bayan takarar Obi a ADC.
Sai dai hakan ya janyo martani daga magoya bayan Atiku, lamarin da ya kara rarraba kawuna a cikin hadakar tare da tayar da shakku kan dunkulewar adawa gabanin zaben 2027.
