Hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Temitope Ajayi, ya mayar da martani ga tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, kan ikirarin cewa Shugaba Tinubu bai taimaka wa Buhari ya zama shugaban kasa ba a 2015.
A wata wallafa da ya yi a shafinsa na sada zumunta, Ajayi ya bayyana cewa duk da Buhari na da kuri’un Arewa miliyan 12, ya sha kasa a zaben shugaban kasa sau uku – a 2003, 2007 da 2011 – kafin 2015.
Daily Nigerian ta ruwaito hadimin na Tinubu na cewa “da babu goyon bayan Tinubu a zaben fidda gwani na APC a 2014, Buhari ba zai samu tikitin takarar shugaban kasa ba”.
Ajayi ya zargi Boss Mustapha da rungumar mantuwa da tarihi, yana mai cewa bai kamata a rage darajar gudunmawar da Tinubu ya bayar wajen samun nasarar Buhari ba.
