Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaBa kwadayin mulki ne ke saka Peter Obi yawan takara ba a...

Ba kwadayin mulki ne ke saka Peter Obi yawan takara ba a Nijeriya – Chimamanda Adichie

Fitacciyar marubuciyar nan, Chimamanda Ngozi Adichie, ta bayyana cewa goyon bayanta ga dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, yana da nasaba da yadda ta ke ganin jajircewarsa da kishinsa ga ci gaban Najeriya.

A wata hira ta musamman da aka yi da ita a da gidan talabijin na Channels, Adichie ta ce Obi ya bambanta da yawancin ‘yan siyasa, domin ba girman kai ko kwadayin mulki ke tura shi yin takara ba.

Akwai mutane da dama da ke neman mulki saboda girman kai, ba don suna da wata niyyar gyara kasar ba” in ji Chimamanda.

Chimamanda ta kara da cewa dabi’un Obi na kaskantar da kai, gaskiya da rikon amana, suna daga cikin abubuwan da suka bambanta shi da sauran ‘yan takara.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata