Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaBa na dauke da fushin kowa a zuciya ta - Goodluck Jonathan

Ba na dauke da fushin kowa a zuciya ta – Goodluck Jonathan

Tsohon shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan, ya bayyana cewa baya rike da kowa a zuciyarsa dangane da wani abu da ya faru a baya, walu a siyasa ko ga mutuncin sa.

Jonathan ya jaddada cewa yafe wa kowa, don haka ya na da kyau ’yan ƙasa su rungumi waɗannan dabi’u na yafiya.

Ya yi wannan jawabi ne ranar Laraba a Abuja, yayin bikin addu’ar tunawa da tsohon Ministan Noma da Cigaban Karkara, Audu Ogbeh, wanda ya rasu kwanan nan.

Jaridar Punch ta ruwaito wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ikechukwu Eze, ya fitar, inda ya fassara marigayin da mutum mai sauƙi kai da yafiya, akidar da ya ce zai yi koyi da ita.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata