Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiBa rauni ne zai sa mu yi sulhu da 'yan bindiga ba...

Ba rauni ne zai sa mu yi sulhu da ‘yan bindiga ba – Gwamnatin jihar Sokoto

Gwamnatin jihar Sokoto ta kare matakin da ta dauka na neman yin sulhu da ‘yan bindiga da suka amince da ajiye makamansu, inda ta bayyana hakan a matsayin mafita mai dorewa ga matsalar tsaro a jihar.

Gwamnatin na mayar da martani ne kan kalaman da wani mai sharhi kan shafukan sada zumunta, Basharu Altine Guyawa ya yi, wanda ya soki matakin.

A wata sanarwa da mai baiwa gwamna Ahmed Aliyu shawara kan harkokin tsaro, Kanar Ahmed Usman mai ritaya ya fitar, ya ce ba rauni ne ya sa gwamnati neman sasanci ba.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata