Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya ce dorewar zaman lafiya ba ta taƙaitu ga matakan tsaro kaɗai ba, sai dai ta haɗa da ci gaba, haɗin kai da samar da damar tattalin arziki ga al’umma. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin kaddamar da gidaje, titin kwalta mai tsawon kilomita shida, Cibiyar Lafiya ta Matakin Farko da kuma Cibiyar Koyon Sana’o’i a Tudun Biri, Jihar Kaduna.
A cewar Gwamnan, an zaɓi Tudun Biri a matsayin wurin aiwatar da shirin ne bayan harin bama-baman kuskure da ya kashe fararen hula a watan Disambar 2023.
Ya bayyana cewa umarnin da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar ya haifar da tsarin ci gaba na haɗin gwiwa wanda ya wuce taimakon gaggawa zuwa cikakken sake gina rayuwar al’umma, ta hanyar samar da gidaje na zamani tare da muhimman ababen more rayuwa domin zaman lafiya mai ɗorewa.
Gwamna Uba Sani ya ce Gwamnatin Jihar Kaduna ta taka muhimmiyar rawa tun daga farkon aukuwar lamarin har zuwa kammala ayyukan sake gina Tudun Biri. Ya ƙara da cewa an yi amfani da wasu filayen noma wajen gina gidaje da ababen more rayuwa, inda aka tattauna da manoma da abin ya shafa tare da tallafa musu ta hanyar samar da kayan aikin noma, shirye-shiryen koyon sana’a da hanyoyin dogaro da kai.
Ya ce tun da farko gwamnati ta samar da kulawar gaggawa ta lafiya da tallafin walwala, sannan daga baya aka faɗaɗa mayar da hankali kan lafiya, ilimi, ababen more rayuwa da hanyoyin samun kuɗi, bisa manufar cewa jihar ba za ta amince da kafa sansanonin ‘yan gudun hijira ba.
Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta gina Cibiyar Lafiya mai gadaje 25 a Tudun Biri, wadda ke bayar da ire-iren kiwon lafiya guda biyar ciki har da kula da mata masu juna biyu, ƙananan tiyata da kula da cututtukan ido.
Haka kuma an gina titin kwalta mai tsawon kilomita shida da ke haɗa al’ummar da hanyar Filin Jirgin Sama na Kaduna, tare da fifita mazauna Tudun Biri a shirye-shiryen tallafin gwamnati, raba takin zamani, shinkafa da masara, da kuma kafa Cibiyar Koyon Sana’o’i domin matasa. A fannin ilimi kuwa, an gina sabuwar makarantar firamare tare da goyon bayan Rundunar Sojin Najeriya da abokan hulɗar ci gaba.

