DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 10, 2026
HomeLabaraiBa za a dawo daukar fasinjojin Kaduna-Abuja ba har sai mun tabbatar...

Ba za a dawo daukar fasinjojin Kaduna-Abuja ba har sai mun tabbatar da komi ya koma dai-dai – Hukumar kula da jiragen kasa ta Nijeriya

Hukumar kula da jiragen kasa ta Njeriya NRC ta bukaci ma’aikatanta da ke aiki a layin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna da su bi doka da ƙa’idojin aiki cikin tsanaki, musamman bayan hadarin da ya faru da jirgin a ranar 26 ga Agusta, 2025.

Babban Daraktan hukumar Dr. Kayode Opeifa ne, ya bayyana haka ne a Lagos a ranar Juma’a, yayin da yake gabatar da sakamakon binciken da aka gudanar kan hatsarin.

Ya ce kafin a dawo da jigilar fasinjoji, dukkan ma’aikatan za samu horo na musamman na kwanaki hudu daga ranar Litinin, 22 ga Satumba, domin tabbatar da tsaro da ingancin aikinsu.

A cewarsa ba za a fara jigilar fasinjoji ba har sai an tabbatar da komai ya koma daidai.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata