Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiBa za mu yi bushasha a bikin cika shekaru 65 da samun...

Ba za mu yi bushasha a bikin cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai ba – Gwamnatin Najeriya

Ministan yada labarai da wayar da kai na Najeriya Alhaji Muhammad Idris ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba za ta yi bushasha a bikin cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai ba.

Ministan ya yi wannan jawabi ne a wani taron manema labarai a Abuja, gabanin taron bikin tunawa da ranar ‘yancin kai, wanda za a gudanar a ranar 1 ga watan Oktoba mai kamawa, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Idris ya ce za a gabatar da wasu al’amura da suka hadar da addu’o’i bayan sallar Juma’a da kuma bayan gabatar da ibada ranar Lahadi, sai kuma muhawara tsakanin dalibai.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata