Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiBaba ya koyar da mu kada mu ci hakkin kowa - Diyar...

Baba ya koyar da mu kada mu ci hakkin kowa – Diyar Buhari Nana

Hadiza Mohammed, daya daga cikin ‘ya’yan tsohon shugaban kasa marigayi Muhammadu Buhari, ta bayyana cewa mahaifinsu ya horar da su da tarbiyyar gaskiya da amana, tare da hana su daukar abin da ba nasu ba.

A wata tattaunawa da manema labarai a gidansu na Daura, Hadiza, wanda aka fi sani da Nana, ta tuna wani lokaci a yarinta da ya koyar da su wani darasin rayuwa mai karfi.

Jaridar The Guardian ta ambato diyar marigayin ta ce wannan darasi ya koya musu kada su ci kwabon kowa, kuma suna godewa Allah da tarbiyyar da suka samu daga wurin mahaifinsu.

Ta kuma bayyana Buhari a matsayin mutum mai saukin rayuwa, ba mai son duniya ba, kuma Musulmi mai tsoron Allah har zuwa karshen rasuwarsa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata