Babban layin wutar lantarki na ƙasa ya fadi Litinin din nan, lamarin da ya jefa ’yan Nijeriya da dama cikin duhu bayan da manyan tashoshin samar da wuta suka daina aiki.
Jaridar PUNCH, ta rawaito cewa wakilinta cewa layin wutar ya faɗi kusan ƙarfe 3:00 na rana, a daidai lokacin da samar da wutar lantarki ya ragu matuƙa a fadin ƙasar.
Bayanan da aka samu sun nuna cewa samar da wuta ya kai kimanin megawatt 4,800 tun da safiyar Litinin, amma daga bisani ya faɗi ƙasa zuwa megawatt 139 zuwa ƙarfe 3:00 na rana.
