Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiBabu inda aka yi son-rai wajen zaben jami’an da za su yi...

Babu inda aka yi son-rai wajen zaben jami’an da za su yi wa alhazai hidima a hajjin 2025 – NAHCON

Hukumar kula da hajji ta Nijeriya NAHCON ta nesanta kanta daga zargin cin hanci da rashawa a cikin tsarin zaben tawagar likitocin da za ta kula da masu aikin hajji na shekarar 2025.

Jaridar Daily Nigerian ta ba da labarin cewar ana zargin NAHCON da yin wata kumbiya-kumbiya wajen zaben ma’aikatan wucin gadi da za a tura Saudiyya don aikin Hajjin bana.

Sai dai hukumar, cikin wata sanarwa da Shafii Sani-Mohammed ya sanya wa hannu, jami’in yada labarai a hukumar, ta musanta aikata duk wani ba daidai ba da ake zargi, tana mai jaddada cewa ana gudanar da aikin ne karkashin wani kwamiti na musamman wanda manyan jagororinsa suka fito daga kwararri a fannin lafiya, ba na hukumar NAHCON ba.

muhammad kabir
muhammad kabirhttps://dclhausa.com
Muhammad Kabir, ƙwararren ɗan jarida ne wanda ke da gogewa a fannin yada labarai na zamani (Digital Media)...
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata