Ma’aikatar gidaje da bunƙasa birane ta tarayya ta musanta jita-jitar da ke yawo cewa gwamnatin tarayya ta fara shirin sayar da gidaje 753 da hukumar EFCC ta kwace daga tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele.
A wata sanarwa da Daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar, Badamasi Haiba, ya fitar a Abuja ranar Asabar, an bayyana cewa gwamnati ba ta amince da wani kamfani ko wani mutum ba domin aikin sayar da gidajen.
EFCC ta mika mallakar gidajen ga ma’aikatar gidaje a watan Mayun 2025, kuma ministan gidaje, Ahmed Dangiwa, ya ce gwamnati za ta sayar da gidajen ta hanyar da ta dace, karkashin shirin Renewed Hope Agenda na Shugaba Bola Tinubu.
Sai dai ma’aikatar ta yi gargaɗi cewa babu wani tsarin sayarwa da aka fara, kuma duk wanda ke sha’awar sayen gidajen ya jira sanarwa daga gwamnati.
