Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiBabu wanda ya hana Kasshim Shettima shiga fadar Shugaban kasa ta Villa,...

Babu wanda ya hana Kasshim Shettima shiga fadar Shugaban kasa ta Villa, labarin ba ya da tushe bare makama – Mai magana da yawunsa Stanley Nkwocha

Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai Stanley Nkwocha,ya bayyana labarin da ke yawo a kafafan sada zumunta, dangane da hana Kashim shettima shiga ofishin shugaban kasa a matsayin labari mara tushe bare makama,face son batawa fadar shugaban kasa suna.

Sanarwar Stanley dai ta rawaito cewa an ta yada labarin cewa akwai wani sojoji da aka girke suka hana mataimakin shugaban kasa Kasshim Shettima shiga fadar Shugaban kasa.

Sanarwa ta kara da cewa ba wani sabon abu bane, domin kuwa ko a farkon wannan makon, an ta yada hotunan allunan yekuwar yakin neman zaben Shugaba Tinubu da Kasshim wanda tuni Fadar Shugaban Kasar ta fito karara ta musanta.

Stanley Nkwocha ya kuma kara da cewa, Mataimakin shugaban kasar ya ci gaba da maida hankali kan ayyukansa,da kuma marawa shugaban kasa baya wajen cimma muradun ‘yan Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata