Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa babu waninmakirci da zai yi nasara akan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027, kuma ba zai fuskanci irin kalubalen siyasa da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya samu ba.
A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Anietie Ekong, ya fitar ranar Lahadi, Akpabio ya ce yankin Niger Delta ba zai yarda da kowanne shiri na kayar da Tinubu daga mulki ba.
Yayin da yake jawabi a wajen bikin cikar hukumar raya yankin Neja Delta NDDC shekaru 25 a birnin Port Harcourt, Akpabio ya ce mutanen yankin suna goyon bayan sake tsayawar Tinubu a 2027 saboda ayyukan raya kasa da ya aiwatar a yankin.
