Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiBabu wata tsama tsakanin Tinubu da Buhari, kansu hade yake - Garba Shehu

Babu wata tsama tsakanin Tinubu da Buhari, kansu hade yake – Garba Shehu

Mai magana da yawun tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari, Garba Shehu, ya karyata jita-jitar da ke yawo cewa akwai sabani tsakanin tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari da shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Trust TV a ranar Litinin, Garba Shehu ya bayyana cewa babu wata takaddama a hukumance tsakanin shugabannin biyu, yana mai cewa dukkansu har yanzu suna karkashin inuwa daya ta jam’iyyar APC.

Garba Shehu ya jaddada cewa tsohon shugaban kasa Buhari na ci gaba da biyayya ga jam’iyyar APC wadda ta ba shi damar zama shugaban kasa bayan kasa sau biyu a baya.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata