Thursday, April 9, 2026
HomeLabaraiBan damu da korata ba amma dai Aisha Binani ce ta ci...

Ban damu da korata ba amma dai Aisha Binani ce ta ci zaben gwamnan Adamawa – Tsohon kwamishinan zabe Hudu Ari

Kasa da sati daya da majalisar tarayya ta amince da korar tsohon kwamishinan zaben hukumar INEC a jihar Adamawa Barista Hudu Ari, ya nace kan cewa ‘yar takarar jam’iyyar APC Sanata Aisha Dahiru Binani ce ta ci zaben gwamna da aka yi a 2023.

An dai dakatar da Barista Hudu Ari ne saboda ya ayyana Binani a matsayin wadda ta ci zabe ana tsaka da kirga kuri’u.

Sai dai a wani taron manema labarai da yayi a Bauchi, ya yi rantsuwa da Alkur’ani cewa yana da shaidun da za su tabbatar da cewa Aisha Binani ta kayar da Gwamna mai ci Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP.

 

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata