Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiBankin CBN ya kaddamar tsarin BVN ga 'yan Nijeriya mazauna kasashen waje

Bankin CBN ya kaddamar tsarin BVN ga ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje

By Salim Muhammad Gali

Babban bankin Nijeriya CBN tare da haɗin gwiwar Hukumar NIBSS da ke kula da harkokin bankuna a Nijeriya sun ƙaddamar da sabon tsarin da zai bai wa ‘yan Nijeriya da ke zaune a kasashen ƙetare damar samun BVN ba tare da sun koma gida Nijeriya ba.

Gwamnan Babban bankin kasar CBN, Olayemi Cardoso, ne ya ƙaddamar da shirin a Abuja.

Cardoso ya bayyana cewa tsarin zai sauƙaƙe tare da ƙarfafa tsarin hada-hadar kuɗin Najeriya, hakam ana hasashen tsarin za a yi hada-hadar da ta kai dala bilyan 1 a kowane wata.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa sabon tsarin zai ba da damar rijista ta yanar gizo ta amfani da fasahohin zamani kamar tantance fuska, takardun shaidar zama ɗan Najeriya da sauran matakan tsaro, tare da tabbacin kariyar bayanai.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata