Babban Bankin Nijeriya, CBN, ya ƙara tsaurara matakan da yake ɗauka kan masu wulakanta takardar kuɗin Naira, inda ya yi gargaɗi ga ‘yan ƙasa da su daina liƙin kuɗi a wuraren bukukuwa, lalata su, yin jabun kuɗi ko kuma safararsu ba bisa ka’ida ba.
Bankin ya bayyana hakan ne a wajen Baje Kolin Kasuwanci na Ƙasa da Ƙasa na Kaduna, inda ya kuma yi bayani kan muhimman nasarorin da aka samu a ƙarƙashin shirye-shiryen gyaran da yake aiwatarwa.
Mataimakiyar Darakta a Sashen Hulɗa da Jama’a da Zuba Jari ta CBN, Mrs. Sidi Ali Hakama, ta ce girmama Naira wajibi ne a doka da ta ƙasa, tana mai bayyana kuɗin a matsayin alamar martabar Nijeriya.
Ta samu wakilci daga Mataimakin Darakta a Hedikwatar CBN da ke Abuja, Abbas Ibrahim Ahmed.
