Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiBankuna sun kara kuɗin tura saƙo zuwa N6 daga Naira 4 a...

Bankuna sun kara kuɗin tura saƙo zuwa N6 daga Naira 4 a fadin Nijeriya

Bankunan kasuwanci a Najeriya sun ƙara kuɗin tura saƙon SMS zuwa Naira 6, daga Naira 4 da ake biya a baya.

Wannan ƙarin kuɗin na kunshe ne a cikin saƙonnin da wasu bankuna suka aikewa kwastomominsu a safiyar ranar Laraba, kamar yadda rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

Bankunan sun bayyana cewa ƙarin ya biyo bayan hauhawar farashin sadarwa da kamfanonin sadarwa suka sanar a baya-bayan nan.

Sai dai har yanzu CBN bai fitar da wata sanarwa kan matakin ba, yayin da kwastomomi ke bayyana damuwa kan yawan ƙarin kuɗin da suke fuskanta daga bankuna.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata