Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiBan yi nadamar bijire wa Atiku ba kuma hadakar da ya kirkira...

Ban yi nadamar bijire wa Atiku ba kuma hadakar da ya kirkira ba za ta je ko’ina ba – Samuel Ortom

Tsohon Gwamnan Jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayyana cewa bai taba nadamar kin yiwa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar aiki a zaben 2023 ba, duk da cewa a lokacin suna jam’iyya daya.

Ortom ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels, inda ya ce siyasa ba wai yin biyayya ga mutum ko jam’iyya ba ne, amma tsayawa kan muradun jama’a da nuna gaskiya.

Tsohon gwamnan, wanda ya kasance cikin kungiyar G5, ta gwamnoni biyar da suka bijirewa Atiku a zaben shugaban kasa na 2023,  ya kuma bayyana cewa sabuwar hadakar siyasa da Atiku ke jagoranta ba zata kai ko’ina ba, yana mai cewa “mutane sun gane gaskiya kuma sun gaji da siyasar son rai.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata