Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiBarayin daji sun dora harajin miliyan 56 kafin su ba da dama...

Barayin daji sun dora harajin miliyan 56 kafin su ba da dama a yi noma a jihar Zamfara

Manoma a Dan Isa da ke karamar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara, sun ce ‘yan bindiga na yi musu barazana a wannan daminar.

Da yake tabbatar da hakan ga jaridar Daily Trust ta wayar tarho, Hakimin unguwar Malam Hassan Yarima, ya ce ‘yan barayin dakin sun bukaci kauyuka 35 da ke karkashin gundumarsa kowane ya biya Naira 800,000 kafin a bar mazauna yankin su yi noma.

Haka kuma kowane kauye zai biya wata Naira 800,000 don bai wa mazauna garin damar girbe amfanin gonakinsu,wannan ita ce yarjejeniyar da suka cimma da shugaban ‘yan fashin mai kula da wannan yanki, Dan Sadiya.

A cewar Hakimin ba su da wani zabi illa su bi umarninsa, in ba haka ba, ‘yan fashin ba za su bari su yi noman ba.

Sai dai Yarima ya koka cewa duk da biyan kudin noma, har yanzu ‘yan bindiga sun mamaye kauyukan su suna satar dabbobi tare da kwashe kayan abinci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata