Wednesday, April 8, 2026
HomeLabaraiBarayin daji sun halaka mutane 6, sun sace 130 A Katsina cikin...

Barayin daji sun halaka mutane 6, sun sace 130 A Katsina cikin kwanaki uku

‘Yan bindiga sun kashe akalla mutane shida tare da yin garkuwa da mutane 130 a hare-hare daban-daban da suka kai cikin kwanaki uku kacal a karamar hukumar Sabuwa da kewaye, Jihar Katsina.

Rahotanni sun nuna cewa a daren Lahadi, da misalin karfe 11:00 na dare, maharan sun kai farmaki a garin Dankurmi, inda suka shafe kusan awanni hudu suna bi gida-gida. A wannan hari, sun kashe mutum hudu ciki har da wani ƙaramin yaro, sannan suka yi awon gaba da mutane 79.

Shaidu sun ce a wasu gidaje maharan sun sace miji, mata da ‘ya’ya gaba ɗaya, a wasu kuma sai mata da yara kawai suka tafi da su. Baya ga haka, sun kwashe kayan abinci da babura daga gidajen jama’a.

Bayan Dankurmi, maharan sun kai hari a Gamji, inda suka kashe mutum biyu sannan suka yi garkuwa da mutum 31. A Tsaunin Jino, sun sace wasu 27. Sauran kauyukan da suka fuskanci hare-haren sun hada da Unguwar Goje, Unguwar Sani da Zagi-Zagi, inda aka sace mutane da dama, abin da ya kai adadin wadanda ke hannun ‘yan bindiga zuwa kusan 200.

Rahoton ya kara da cewa tun farkon damina, ‘yan bindigar sun yi tayin yarjejeniyar zaman lafiya da al’ummar Sabuwa, inda suka ce za su bari manoma su yi noma cikin kwanciyar hankali. Sai dai jinkirin amincewa ko kin amincewa daga bangaren al’umma ya fusata su, abin da ake ganin ya sa suka ƙara kaimi wajen kai hare-hare.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata