Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiBarayin daji sun yi ajalin askarawan sa kai da gwamnatin jihar Zamfara...

Barayin daji sun yi ajalin askarawan sa kai da gwamnatin jihar Zamfara ta dauka aiki don samar da tsaro

A kalla jami’an tsaro 13, ciki har da ‘yan sanda 2 da ‘yan sa-kai 11, sun rasa rayukansu a harin ‘yan bindiga a ƙauyen Adabka, da ke karamar hukumar Bukkuyum, Zamfara.

Shaidu daga kauyukan sun ce maharan sun farmaki ƙauyen a ranar Juma’a da dare, suka yi garkuwa da wasu mazauna yanking sannan suka yi wa jami’an tsaro kwanton ɓauna yayin da suke bin su domin ceto mutanen.

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta tabbatar da cewa har yanzu ba a iya ɗaukar gawarwakin ba saboda ‘yan bindigar sun tsaya a dajin da ke kusa.

Rahotanni da jaridar TRT Global ta tattaro sun nuna cewa yankin na fama da hare-haren da ake kaiwa akai-akai duk da yarjejeniyoyin sulhu da gwamnati ta yi da ‘yan bindigar, amma suna karya su suna ci gaba da kai hare-hare.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata