‘Yan bindiga sun kai mummunan hari a kauyen Kurawa, karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto, inda suka halaka mutane uku ciki har da dagacin kauyen.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12 na dare, inda maharan suka kai farmaki bayan sun rushe katangar da mutane suka yi a matsayin kariya daga hare-hare.
Wani mazaunin yankin ya shaida cewa sun samu bayani daga wani kauye a makwabta cewa ‘yan bindiga na kan hanyarsu zuwa Kurawa, inda suka hanzarta sanar da hukumomin tsaro.
Duk da haka, bayan da ‘yan bindigar sun shiga kauyen, suka fara harbe-harbe na kusan mintuna 30, inda jami’an tsaro da vigilante suka yi ƙoƙarin fatattakar su.
Sai dai duk da hakan, dagacin garin, Hussaini Alhaji Yawalle, da wasu mutum biyu sun mutu a harin.
