Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da sake daura damarar kawo karshen matsalar tsaro bayan harin da aka kai kauyen Unguwan Mantau a karamar hukumar Malumfashi, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 13 yayin sallar Asuba.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kai harin ne a matsayin ramuwar gayya bayan da al’ummar kauyen suka yi musu kwanton-bauna kwanaki biyu baya, inda suka yi ajalin da dama daga cikinsu, suka kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su, tare da kwace babura uku da bindigogi AK-47 guda biyu.
Kwamishinan tsaro na cikin gida, Dr. Nasir Mu’azu, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun isa yankin domin dawo da zaman lafiya, tare da tura sojoji da ’yan sanda don fatattakar ’yan bindigar da ke fakewa da amfanin gona a lokacin damina.
