Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiBello Turji na cikin matsin lamba daga sojojin Nijeriya - Minista Badaru

Bello Turji na cikin matsin lamba daga sojojin Nijeriya – Minista Badaru

Ministan Tsaro na Najeriya, Muhammad Badaru, ya bayyana cewa shugaban ‘yan ta’adda Bello Turji yana gudun hijira sakamakon hare-haren da sojojin Najeriya ke kai wa a ‘yan kwanakin nan.

A cewarsa, rundunar soji ta samu nasarar kashe wasu daga cikin manyan shugabannin ‘yan ta’adda da suka hada da:

Maza Barume Madaro da Kachalla Alhaji Dati da Bani Wala Burki da Kachalla Dogo Kwaden da Chairman Hanazuma sai kuma Kachalla Bandiyo da Maiyara Madaci da sauransu.

Minista Badaru ya ce dakarun soji na ci gaba da murkushe ‘yan ta’adda, kuma yawancin shugabanninsu suna cikin firgici da gudu.

Ya kara da cewa sojoji na kara kaimi wajen tattara bayanan sirri domin hana hare-haren ta’addanci kafin su faru.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata