Wannan asara ta samu be sakamakon wasu manufofin gwamnati da suka haddasa faduwar farashin kayayyaki, sai kuma dogaro da hasashen yanayi daga hukumar kula yanayi ta Nijeriya NIMET da dai sauran su.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kungiyar Foundation for Peace Professionals ta fitar, inda ta bayyana cewa fannin noma a Nijeriya na fuskantar babbar matsalar da ke barazana ga samar da abinci.
Daraktan Abdulrazaq Hamzat, ya ce asarar da aka kiyasta na nufin manoma da dama sun rasa jarinsu a wannan yanayi da gwamnati ta shigo da sabbin tsaruka da suka karya kayayyakin da ake nomawa a cikin gida.
