Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiBiyayyarka tana ga ‘yan Nijeriya ne ba gwamnati ba- Hudubar Jam’iyyar ADC...

Biyayyarka tana ga ‘yan Nijeriya ne ba gwamnati ba- Hudubar Jam’iyyar ADC ga Sabon Shugaban INEC

Jam’iyyar adawa ta ADC ta bayyana matsayarta kan nadin Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon shugaban hukumar zabe ta Nijeriya INEC wanda Shugaba Bola Tinubu ya gabatar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar, Bolaji Abdullahi ya fitar a ranar Alhamis bayan bayyana Joash a matsayin sabon shugaban hukumar, ya ce za su ba sabon shugaban hukumar damar nuna kwarewarsa wajen gyara tsarin zabe.

Jam’iyyar ta ce tana sa ran Farfesa Amupitan, wanda masani ne a fannin shari’a, zai dawo da martabar hukumar da kuma yarda tsakanin ‘yan kasa da idon duniya wajen gudanar da sahihan zabubbuka a Nijeriya.

Haka kuma ya kara da cewa, ya kamata sabon shugaban INEC ya san cewa biyayyarsa tana ga al’ummar Nijeriya, ba gwamnati ba kamar yadda Channels TV ta wallafa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata