Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiBuhari mutum ne mai girmama al'adu da masarautu - Sarkin Musulmi

Buhari mutum ne mai girmama al’adu da masarautu – Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya shiga sahun wadanda ke jimamin rasuwar tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a wani asibiti a birnin London ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025.

A cikin sakon ta’aziyya da tawagar yada labaran Sarki ta fitar a ranar Litinin, Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana rasuwar Buhari a matsayin “karshen wani zamani,” inda ya jaddada halayen da aka san shi da su na ladabi, kishin kasa da hidima ga al’umma.

“Ina mai tabbatar da cewa Marigayi Buhari shugaba ne na Najeriya, wanda Allah Ya hore masa halaye masu kima da suka sa ake girmama shi kafin, lokacin da kuma bayan shugabancinsa,” in ji Sarkin Musulmi.

Shugaban na Daular Usmaniyya ya kuma yaba da yadda Buhari ke mutunta al’adu da masarautu tare da kokarinsa wajen gina zaman lafiya da hadin kai a fadin kasar.

Ya tuna lokacin da Buhari ya zama Shugaban kasa na mulkin soja, lokacin da ya kaddamar da yakin da rashin da’a (War Against Indiscipline), da kuma yadda ya taka rawa wajen kafa matatun mai a matsayinsa Ministan Man Fetur.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata