Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afirka (CAF) ta sanar da dakatar da kocin tawagar ƙasar Senegal, Pape Thiaw, daga aikinsa na ɗan lokaci.
A cikin wata sanarwa da CAF ta fitar, hukumar ta tabbatar da matakin dakatarwar, sai dai ba ta bayyana dalilan dakatarwar ba a wannan lokaci.
Pape Thiaw dai shi ne kocin da ke jagorantar tawagar Teranga Lions, kuma dakatarwar na zuwa ne a lokacin da Senegal ke shirin buga wasu wasannin ƙasa da ƙasa.
