Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiCikin makonni 28 cutar Lassa ta yi ajalin mutane 152 a Najeriya...

Cikin makonni 28 cutar Lassa ta yi ajalin mutane 152 a Najeriya – NCDC

Hukumar dakile cututtuka ta Nijeriya NCDC ta bayyana cewa mutane 152 ne suka rasu sanadiyyar cutar Lassa a cikin makonni 28 na shekarar 2025.

Rahoton baya-bayan nan na hukumar ya ce an tabbatar da mutum 811 da suka kamu da cutar a jihohi 21 da kananan hukumomi 105, inda mafi yawan su ke a Ondo, Edo, Bauchi, Taraba da Ebonyi.

Daily Nigerian ta ruwaito NCDC ta ce kodayake yawan masu kamuwa ya ragu idan aka kwatanta da shekarar 2024, amma adadin mace-mace ya karu daga kashi 17.3% zuwa 18.7%.

An danganta ƙarin mace-macen da jinkirin zuwa asibiti da ƙarancin samun magani cikin lokaci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata